Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargadi cewa kusan mutane biliyan ɗaya ke fama da matsalolin tabin hankali, tana mai kira ga gwamnatoci su ɗauki matakai masu ƙarfi don magance wannan barazana.
Shugaban WHO, Dakta Tedros Ghebreyesus, ne ya bayyana haka kafin babban taron koli kan cututtukan da ba sa yaduwa da matsalolin tabin hankali da za a gudanar a ranar 25 ga Satumba.
Ya ce rashin ɗaukar mataki kan waɗannan matsaloli zai jawo mutuwar mutane da dama tare da jefa tattalin arzikin ƙasashe cikin cikas.
A cewarsa, cututtuka da ba sa yaduwa sun haɗa da bakwai daga cikin manyan abubuwan da ke jawo mutuwa a duniya, sannan ƙarin kusan biliyan ɗaya na fama da matsalolin tabin hankali.
Ya kuma nuna damuwa cewa kisan kai shi ne na uku a jerin abubuwan da ke jawo mutuwar matasa a duniya.
Dakta Ghebreyesus ya ce matsalolin tabin hankali da cututtuka da ba sa yaduwa ba wai kawai suna jawo asarar rayuka ba, har ma suna ɗauke da nauyin zamantakewa da tattalin arziki mai girma.
Ya ƙara da cewa kisan kai na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke jawo mutuwar matasa masu shekaru 15 zuwa 29, inda kaso 73 cikin 100 na faruwa a ƙasashe masu ƙaramin da matsakaicin tattalin arziki.
A Najeriya kuwa, a watan Janairun 2024, adadin mace-mace sakamakon kisan kai ya kai 3.5 cikin 100,000 na jama’a, wanda ya kai kimanin mutane 15,000 ke rasa rayukansu a duk shekara.
Ya bayyana cewa ƙasashe sun shafe shekara guda suna tattaunawa kan wata sanarwar siyasa da za a kammala a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA), wacce ta ƙunshi muhimman manufofi kafin shekarar 2030.
Wannan ya haɗa da rage masu amfani da taba da miliyan 150, faɗaɗa samun damar kula da matsalolin tabin hankali ga miliyan 150, da tabbatar da cewa miliyan 150 sun samu ikon magance hawan jini.
Shugaban WHO ya jaddada cewa saka hannun jari a fannin rigakafin cututtuka ba asara ba ne, yana mai cewa “yana daga cikin mafi kyawun shawarar tattalin arziki da kowace gwamnati za ta iya ɗauka.”
Ya ce duk da haka, gwamnatoci kan fuskanci ƙalubale daga masana’antu masu cin moriyar sayar da kayayyakin da ke cutar da lafiya.
Ya nanata cewa, ƙasashen da suka ɗauki mataki cikin gaggawa za su ceci rayuka da dama, su kare iyalai, su rage kuɗaɗen jinya, kuma su buɗe ƙofofin bunƙasar tattalin arziki.
Babban taron koli na UNGA ana sa ran zai samar da wani ƙuduri mai ƙarfi da zai jagoranci haɗin gwiwar ƙasashe wajen yaki da cututtukan da ba sa yaduwa da kuma faɗaɗa kulawa ga masu fama da matsalolin tabin hankali a shekaru goma masu zuwa.













































