Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta naɗa Alhaji Alidu Shutti a matsayin Sakataren riƙo kwarya, bayan murabus ɗin Dr. Abdullahi Kontagora a ranar 6 ga Disamba.
Shutti, wanda ya riƙe mukamin Daraktan Bincike da Daidaitawa tun 2023, ya yi aiki da NAHCON tun 2007, inda ya rike mukamai da dama, ciki har da Shugaban Sashen Masu Shirya Tafiya da Mataimakin Mai Kula da Ofishin Makkah.
Ya na da ƙwarewa a Harkokin Hajji tare da shaidun karatu a Mulki, Nazarin Addinin Musulunci, da Jarida, kuma ya halarci tarukan horaswa a ƙasashe da dama. Ana sa ran ƙwarewarsa za ta taimaka wajen nasarar Hajjin 2025.