Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara a ranar Talata ta tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga sun kai wani mummunan hari a garin Ilesha-Baruba a yankin arewacin jihar, inda suka kashe mutane bakwai ciki har da wani dan banga.
Rundunar ‘yan sandan ta kuma ce, ‘yan sanda sun kama wani mai ba da labari mai alaka da kungiyar ‘yan bindigar, duk da cewa sun kara kaimi wajen kai hare-hare a yankunan da lamarin ya shafa.
Kakakin rundunar, Toun Ejire-Adeyemi, ya ce rundunar ta ce tana gudanar da bincike kan wasu munanan abubuwa guda biyu da suka faru a ranar Lahadi a kananan hukumomin Baruten da Kaiama na jihar.
“Da misalin karfe 21:30 ne wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne, wadanda adadinsu ya kai goma, suka dira a tashar mota ta Ilesha – Baruba, inda suka bude wuta ba kakkautawa a kan jama’ar da suka taru a wurin shakatawa da ke kusa da wurin, a sakamakon haka, mutane shida wadanda aka bayyana sunayensu kamar su Alhaji Ja’awire, AbdulJabar, Mohammed Nasamu, da wasu mutane uku suka rasa rayukansu, yayin da wasu biyu suka samu munanan raunuka daga harbin bindiga.
“An ajiye wadanda suka mutu a dakin ajiye gawa na Ilesha Baruba, yayin da wadanda suka jikkata ke karbar magani, an fara gudanar da bincike, kuma an aiwatar da cikakken matakan tsaro don tabbatar da an gurfanar da wadanda suka aikata laifin gaban kuliya.
Rundunar, ta kuma bukaci mazauna yankunan da su baiwa jami’an tsaro hadin kai, inda ta yi gargadin cewa duk wanda ya taimaka ko kuma ya aikata laifuka a kowane bangare na jihar zai fuskanci fushin doka.