Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta ba da umarnin a kwace dala miliyan 4.7, da miliyan 830, da wasu kadarori masu yawa da ke da alaka da tsohon gwamnan babban bankin kasa (CBN), Godwin Emefiele.
Mai shari’a Yellim Bogoro a cikin hukuncin da ya yanke ranar Juma’a ya kuma ba da umarnin a kwace hannun jarin da ya kai dala 900,000 ga daya daga cikin makusantan Emefiele, Anita Joy Omoile.
Karin labari: Gwamnatin Tarayya Ta Gurfanar Da Emefiele Kan Sabbin Laifuka 20
Kotun ta kuma bayar da umarnin a kwace wani hannun jarin da ya kai Dala Miliyan 4.4 na kamfanin Deep Blue Energy Services Ltd da kuma wasu kudi Naira miliyan 283 a bankin Zenith da aka gano a Liman Investment Ltd, da €20,000, da £1,999.50, wanda ya samo asali daga kamfanin hada hadar Canjin kudi na Exactquote Bureau De Change (BDC) da dukkanin kamfanonin da ke da alaka da Omoile.
Daga karshe mai Shari’a Bogoro ya bukaci a mikawa gwamnatin tarayya dukkan kudaden da aka kwato bayan da aka mallake su ba bisa ka’ida ba.