Masu ba da shawarwari kan aure kuma marubuta, Vincent Hope da Deborah Vincent, sun kaddamar da littattafai uku da ke da nufin taimakawa matasa wajen shawo kan kalubale a lokacin samartaka, zabin abokin dangantaka da kuma gina aure mai dorewa a ranar Asabar.
Littattafan sun hada da Growing Up: Understanding Yourself, Relationships & Pressure, Finding Your Soulmate da Building a Great Marriage an gabatar da su a wani bikin kaddamarwa a Kano da manyan jami’an gwamnati, masana, ‘yan jarida da sauran baki suka halarta.
SolaceBase ta ruwaito cewa kaddamarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake samun tattaunawa da yawa a fadin kasar kan kalubalen dangantaka, matsalolin aure da kuma dabi’un iyali a Najeriya, inda masu ba da shawara, malamai da shugabannin addini ke kara yin kira da a yi wa matasa bita da jagoranci kafin auren su.
A jawabin sa a taron, Darakta yada labarai kuma mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana littattafan a matsayin wasu matakai da suka dace da za su yi wa matasa jagoranci mai amfani yayin da suke shirin aure.
Ya ce taron ya tuna masa wani lokaci da al’adar karatu ta fi karfi, kuma littattafai suna taka muhimmiyar rawa wajen tsara dabi’u da shirya matasa don bukatun rayuwa.
“A matsayina na wanda yake da aure fiye da daya, na ga kokarin wadannan marubuta wajen kwatanta abin da ke faruwa a cikin al’umma dangane da aure,” in ji shi.
A cewar Dawakin Tofa, daya daga cikin manyan kura-kuran da mutane ke yi shi ne zabar abokin rayuwa da bai dace ba, yana mai jaddada cewa yayin da mutane da yawa ke mayar da hankali kan bikin aure, rike aure cikin nasara shi ne kalubale mafi girma.
A jawabinsa na musamman kan bunkasa kai, Farfesa Aliyu Barau na Jami’ar Bayero Kano BUK, ya bukaci iyalai su koyi hikima, hakuri, karfin zuciya da kuma kyakykyawan tunani wajen magance rikitarwar rayuwar zamani.
Ya ce ma’aurata su yi kokarin fahimtar juna da girmama ra’ayin juna, yana mai bayyana cewa iya sarrafa fushi yana da matukar muhimmanci wajen warware rikici da kiyaye dangantaka mai kyau.
Barau ya bayyana aure a matsayin dadaddiyan tsari kuma mafi juriya a cikin al’umma, yana mai kira ga mutane na kowane addini, kabila da al’adu su kare shi domin tsararraki masu zuwa.
Daya daga cikin marubutan, Vincent Hope, ya ce sun rubuta littafan uku ne bayan shekaru masu yawa suna ba da shawara ga mutane da iyalai, kuma manufarsu ita ce samar wa mutane ilimi mai amfani ta hanyar littattafai da kuma dandalin yanar giwo.
Ya bayyana cewa littafin ‘Growing Up’ yana magana ne kan kalubalen da matasa ke fuskanta yayin shiga matakin samartaka, yayin da ‘Finding Your Soulmate’ ke taimakawa matasa wajen yin zabin abokin rayuwa cikin sanin yakamata, cikin halin rashin jin dadin da ake ciki na dangantaka.
Hope ya ce an rubuta littafin ‘Building a Great Marriage’ ne domin magance gibin ilimi da ke haifar da rikici a cikin aure.
“Aure ba yaudara ba ne., abin da ke zama yaudara shi ne lokacin da mutane suka yi aure ba tare da ilimin da ya dace ba,” in ji shi.
Haka kuma, Deborah Vincent, wacce babbar ‘yar jarida ce da ke aiki a gidan Talabijin na Channels, ta ce abin da ya zaburar da su wajen rubuta littattafan shi ne damuwa kan yadda al’umma ke tafiya da kuma imanin cewa gidaje masu kyau sune ginshikin kasa mai zaman lafiya da ci gaba.













































