Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta kara wa jami’ai 80 da Kwamishinoni 13 girma

PSC

Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda (PSC) ta amince da kara wa Kwamishinonin ‘Yan Sanda 13 mukami zuwa mataimakan Sufeto Janar (AIGs) da kuma wasu manyan jami’ai 80 zuwa mukamai na gaba.

Shugaban sashen bayanai da hulda da Jama’a na hukumar, Mr Torty Kalu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Laraba a Abuja.

Kalu ya ce an kara wa manyan jami’an girmane bayan sun yi nasara a jarabawar da suka rubutu da kuma tantancewar da hukumar ta gudanar.

Ya kuma ce amincewa da karin girman na daga cikin manyan abubuwan da hukumar ta yanke shawara a taronta.

Ya lissafa sunayen kwamishinonin da aka kara wa girma 13 da suka hada da Itam Obono, Bassey Ewah, Osagie Agans-Irabor, Monday Agbonika, Iyamah Adebor, Isa Nda, Akaninyene Ezima da Livingstein Orutugu.

Sauran sun hada da Afegbua Rashid, Edozie Azuka, Haruna Yahaya, Emenari Innocent da Betty Otimenyin.

Mai magana da yawun hukumar ya ce an kara wa Mataimakan Kwamishinan “yan sanda (DCPs) 17 girma zuwa mukamin Kwamishina.

A cewarsa, sabbin Mataimakan Kwamishina 17 da aka kara wa mukamin sun hada da Nelson Nwamanna, Bolanle Murtala, Danbaba Labbo, Ajayi Oluyemi, Oki Oyintare, Ibrahim Zungura, Iya Mohammed, Darma Na’aliyu, Nuruddeen Sabo da Tijjani Murtala.

Sauran su ne Yakubu Mohammed, Ibrahim Usman, Akingbade Adeyinka, Mohammed Ahmed, Samuel Ahmed, Adedeji Taiwo da Zainab Pembi.

Ya kara da cewa an kuma kara wa Kananan Mataimakan Kwamishina (ACPs) 28 girma zuwa mukamin Manyan Mataimakan Kwamishina, yayin da aka kara wa Manyan Sifiritandoji (CSPs) 33 girma zuwa mukamin Kananan Mataimakan Kwamishina.

Kalu ya ce hukumar ta kuma amince da tabbatar da nadin Kananan Mataimakan Kwamishina II (ASPs II) 162 zuwa mukamin Mataimaka na I.

Ya nakalto cewa shugaban hukumar, Mr Hashimu Argungu, na taya wadanda aka kara girma murnar, yana kuma yi musu nasiha su kasance masu gaskiya, adalci da rikon amana a sabbin mukamansu.

Argungu ya kuma bukaci jami’an da su kasance masu nuna kwarewa a halayensu, su kuma kula da lamuran farar hula, musamman na filaye.

“Ku tuna cewa akwai rayuwa bayan gama aiki.
“Ku kiyaye martaba da kima, ayyukanku su fadi ku su wane ne, ba ku da kanku ku fada ba,” in ji Argungu. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here