Gwamna Yusuf ya jagoranci lalata tan 12.2 na miyagun kwayoyi

IMG 20260629 141207 398 scaled 1 750x430

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, tare da Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) da sauran hukumomin tsaro masu alaka wajen lalata tan 12.2 na miyagun kwayoyi, abubuwa kawar da hankali da sauran sinadarai masu hatsari da aka kama a fadin jihar, yayin da ya yi kira ga ‘yan kasa da su kasance a shirye su kuma su rika bayar da rahoton duk wani abu da ake zargi ga hukumomin da suka dace.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Daraktan yada labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Litinin.

Gwamna Yusuf ya yi wannan kiran ne a lokacin wani bikin lalata kwayoyin da NDLEA ta shirya tare da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Kano a Hawan Kalibawa dake Karamar Hukumar Dawakin Tofa.

Da yake wakiltar Gwamnan a wajen, Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya ce nasarar da aka samu sakamako ne na hadin gwiwa tsakanin NDLEA, ‘Yan Sandan Najeriya, Hukuma NSCDC, Sojojin Najeriya, Hukumar Hana Fasakwauri, Hukumar Shige da Fice, Masu Sanya Ido a tsakanin al’umma, ‘Yan sintiri da kuma ma’aikatan gwamnati masu kishin kasa.

Gwamna Yusuf ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na karfafa hada bayanan sirri a tsakanin hukumomi da hadin gwiwa a kan iyaka domin lalata hanyoyin safar miyagun kwayoyi, tare da fadada Aikin “Safe Corridor” domin al’ummomi da yawa a fadin jihar su samu moriya.

Ya kara bayyana cewa ta hanyar Kwamitin Maido da Zaman Lafiya da Gyaran Matasa, gwamnatin jihar ta kama matasa sama da 400 da ake zargi da hannu a laifukan da suka shafi miyagun kwayoyi da fasa-kwauri.

Gwamnan ya yaba da kokarin dukkan masu ruwa da tsaki a yakin da ake yi da shan miyagun kwayoyi, musamman na hukumar shari’a, kan tabbatar da gaggawar da kuma dacewar gurfanar da masu laifi.

A baya can, Kwamandan NDLEA a Kano, CN Dahiru Lawal Yahaya, ya bayyana cewa Babbar Kotun Tarayya da ke Kano, a ranar 16 ga Janairu, 28 ga Afrilu da 15 ga Mayu 2026, ta ba da umarnin baiwa Hukumar damar lalatawa da kona dukkan miyagun kwayoyi da abubuwan da ke kawar da hankali da aka kama masu nauyin kilogram 11,990.427, da aka kwato daga wadanda aka yanke musu hukunci.

Haka ma, Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa Mai Ritaya, wanda DCGN Ningi ya wakilta, ya bayyana godiya ga Gwamnatin Jihar Kano kan goyon bayanta ga Hukumar, musamman kyautar sabbin motocin Hilux guda uku da sauran tallafin kudi da aka bayar kwanan nan domin karfafa ayyukan ta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here