Sojoji sun ceto ragowar mutum 4 da Masu Garkuwa suka tsare tare da marigayi Janar Rabe

HK q w5X0AAXidP 750x430

Dakarun Rundunar Sojin Najeriya sun ceto mutum hudu da aka yi garkuwa da a ci gaba da ayyukan da suke yi na fatattakar wani fitaccen shugaban ’yan bindiga, Kachalla Muhammadu Fulani, da mambobin kungiyarsa a Jihar Katsina.

Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Harkokin na Jihar Katsina, Dr. Nasir Mu’azu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar. Ya ce an samu nasar ceto su ne ta hanyar ci gaba da gudanar da ayyukan soji a yankunan da ake zargin ‘yan ta’addar na gudanar da harkokinsu.

An sanar da sunayen wadanda aka ceto kamar haka: Musa Yakuba, mai shekaru 62, Alhaji Sa’adu Dayi 68, Mukhtar Danja 36 da Salisu Danja 50.

A cewar sanarwar, an tseratar da wadanda abin ya shafa ne a yayin ci gaba da ayyukan tsaro da aka tsara domin bin diddigi da kama shugaban ‘yan bindigar da abokansa.

Ma’aikatar ta ce likitoci sun kula da wadanda aka ceto nan take bayan an ceto su, domin sun samu raunukan harbin bindiga lokacin da suke tsare.

Ta bayyana cewa jami’an tsaro sun riga sun ceto matar marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar a baya, inda ta ce wadanda aka ceto a yanzu suna cikin wadanda aka gani a hoto tare da marigayi jami’in soja.

Gwamnatin Jihar Katsina ta yaba wa Sojan Najeriya da sauran jami’an tsaro kan abin da ta kira jajircewar, kwarewa da sadaukarwa wajen yaki da rashin tsaro.

“Kokarin da suke yi ba tare da gajiyawa ba na ci gaba da haifar da sakamako mai kyau a yakin da ake yi da ‘yan bindiga da garkuwa da mutane a fadin jihar,” in ji sanarwar.

Gwamnatin ta tabbatar wa al’umma cewa jami’an tsaro na ci gaba da bin diddigin Kachalla Muhammadu Fulani da sauran ‘yan ta’addar da ke aikata laifuka a jihar.

Ma’aikatar ta jaddada cewa za a ci gaba da ayyukan da ake yi har sai an kama dukkan wadanda ke da hannu wajen kai hare-hare kan farar hula marasa laifi a gurfanar da su.

Ta sake tabbatar da kudurin gwamnatin Gwamna Dikko Umaru Radda na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, inda ta ce gwamnati za ta ci gaba da aiki tare da jami’an tsaro don hana ‘yan ta’adda samun mafaka a ko’ina a Jihar Katsina.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here