Sanata Muhammad Danjuma Goje, mai wakiltar Gombe ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, ya ki amincewa da tsarin dan takarar maslaha da reshen jam’iyyar APC na Jihar Gombe ya dauka a zaben shekarar 2027.
Inda ya ce tsarin ya saba wa tanade-tanaden Dokar Zabe da ke jagorantar tsayar da ‘yan takara.
Tunatarwa dai, Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, a wani taro da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya jagoranta ranar Lahadi, sun amince da tsohon Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda mai murabus, Mohammed Ahmadu Deba, a matsayin dan takarar maslaha na jam’iyyar a kujerar Sanatan Goje.
Sai dai, a wata sanarwa da mai taimaka masa, Barrister Saidu Muazu Kumo, ya fitar, Goje, wanda ke neman wa’adi na biyar a Majalisar Dattawa, ya nisanta kansa daga wannan tsari, inda bayyana shi a matsayin wanda ke da kurakurai kuma aka kebe wasu.
“Wannan taro na maslaha da aka gudanar ya hada da Gwamna Yahaya da wasu kalilan daga cikin masu neman takara ne kawai, kuma bai hada da dukkan wadanda aka amince da su a matsayin masu neman takara a jam’iyyar ba,” in ji sanarwar.
Tsohon Gwamnan Jihar Gombe ya nace cewa tsarin ya saba wa tanade-tanaden Dokar Zabe da ke jagorantar tsayar da ‘yan takara.
“Tanade-tanaden Dokar Zabe sun fayyace hanyoyi guda biyu bisa doka na tsayar da ‘yan takara daga jam’iyyun siyasa domin mikawa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa gabanin babban zaben shekarar 2027,” in ji shi.
“Wajibi ne a bi wadannan hanyoyin yadda ya kamata domin tabbatar da bin doka da gaskiya a tsarin zabe.”
Ya kara da cewa masu neman takara da dama sun riga sun sayi Fom din Nuna Sha’awa da Tsayawa Takara amma an cire su daga taron.
“Abin lura ne kuma cewa a fadin mazabu daban-daban, masu neman takara da dama sun sayi Fom din nuna sha’awa da tsayawa takara bisa ka’ida, kuma ba su halarci wannan tsarin maslaha da aka gudanar a Gidan Gwamnati ba,” in ji shi.
Kumo ya jaddada cewa, bisa tsarin zabe da ke aiki, dole ne a bi hanyar da ta dace wajen tsayar da ‘yan takara.
“Bisa tsarin zabe da ke aiki a yanzu, za a gudanar da tsarin tsayar da ‘yan takara ne ta hanyar zaben fidda gwani na kai tsaye, wanda INEC da hukumomin tsaro za su sa ido a kansa, a ranar da jam’iyya za ta sanya,” in ji shi.
Ya yi gargadin cewa duk wani yunkuri na dora dan takara ya saba wa doka.
Wannan lamari ya kara janyo fargaba a cikin APC a Jihar Gombe kan daukar tsarin ‘yan takarar maslaha gabanin zaben shekarar 2027.
Tun da farko, guda daga cikin masu neman takarar gwamna a jam’iyyar, Isa Ali Pantami, shi ma ya ki amincewa da Jamilu Isyaku Gwamna a matsayin dan takarar maslaha na APC.
Pantami ya ce maslaha za ta iya zama ingantacciya ne kawai idan duk masu neman takara sun amince da janyewa da kansu.
“Bisa doka, ba za a iya samun maslaha mai inganci ba tare da hada masu neman takarar da suka sayi ko suka cike fom din nuna sha’awa da tsayawa takara ba,” in ji shi.
Da yake kawo Dokar Zabe, Pantami ya cewa hanyoyi biyu ne kawai aka amince da su wajen zaben ‘yan takara.
“A Sashe na 84 (2), an takaita wa jam’iyyun siyasa hanyoyi biyu ne kawai na zaben ‘yan takara. Hanyoyin biyu sune maslaha, inda duk masu neman takara za su amince a rubuce, da kuma zaben fidda gwani na kai tsaye,” ya bayyana.
“Idan ko da dan takara daya ya ki, to dole ne jam’iyya ta koma ga zaben fidda gwani na kai tsaye.”
Pantami ya kuma bukaci magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu yayin da ake nazarin matakin shari’a da za a dauka.
“Ba za mu yi watsi da wannan cin fuska ga tanade-tanaden doka ba,” in ji shi.












































