Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya karbi katin zama halastaccen dan jam’iyyar APC, wadda ke nuni da komawarsa jam’iyyar a hukumance.
Shekarau, wanda tsohon sanatan Kano ta tsakiya ne, ya karbi katin jam’iyyar ne a mazabarsa ta Giginyu a karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano, inda dubban magoya baya suka yi dandazo don shaida karbar katin.
Taron ya samu halattar manyan a siyasa a jihar, ciki harda gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf da kakakin majalisar dokoki ta jihar Kano da sauran mambobin jam’iyyar.
Da yake jawabi a lokacin taron, Shekarau ya bayyana jindadinsa da irin goyon bayan da jam’iyyar da mambobinta suka nuna masa, inda ya tabbatar da baiwa jam’iyyar cikakken goyon baya a matakin jiha da kuma tarayya.
“Na jidadin irin kara da goyon bayan da aka nuna min, na yi alkawarin baiwa wannan jam’iyya gudumma don tabbatar da ci gabanta da hadin-kai.” Inji shi.
Tsohon gwamnan ya bayyana komawarsa jam’iyyar da nufin kara tabbatar da hadin kai a Kano, inda ya kuma bayyana ci gaban a wani mataki na karfafa tsarin jam’iyyar da hadin kai a dukkan matakai.











































