Ma’aikatan hukumar NiMet sun dakatar da yajin aikin bayan gwamnatin tarayya ta sa baki

NiMet 750x430

Ma’aikatan hukumar kula da yanayi ta kasa (NiMET) sun janye yajin aikin da suke yi bayan gwamnatin tarayya ta shiga tsakani.

Ma’aikatan sun shiga yakin aikin ne saboda rashin kyawun yanayin aiki, tare da hana zirga-zirgar jiragen sama a fadin kasar a ranar Alhamis.

Amma bayan wata ganawa da ministan sufurin jiragen sama Festus Keyamo a Abuja, sun janye yajin aikin.

Ma’aikatan sun damu da rashin aiwatar da sabon mafi karancin albashin ma’aikata na kasa, da yin watsi da bukatar shigar da ma’aikatan da ba a ba su alawus-alawus na baya ba, da kuma yin watsi da muhimman shirye-shiryen horarwa da dai sauransu.

Taron ya samu halartar Darakta Janar na NiMET da Jami’an hukumar kula da sufurin Jiragen sama ta Najeriya (NCAA) da kungiyar ma’aikatan sufuri ta kasa, da sauran masu ruwa da tsaki.

Karanta: Kamfanin Air Peace ya dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a fadin Najeriya

Sauran sun hada da hadaddiyar kungiyar ma’aikatan gwamnati, ma’aikatan fasahar kere-kere da na ma’aikatan gwamnati, kungiyar kwararrun ma’aikatan sufurin jiragen sama, da kungiyar ma’aikatan sufurin jiragen sama ta kasa, da dai sauransu.

Ayyukan jirage sun tsaya cak a filayen jirgin saman yankin sakamakon yajin aikin da ma’aikatan NiMET suka yi.

Yajin aikin da ya kwashe kwanaki biyu ana yi, ya sa fasinjojin da ke jiran jirgin da aka tsara tashin su yin jinkiria filin jirgin saman Nnamdi Azikwe, Abuja; Murtala Muhammed International Airport, Lagos da sauran su.

Kamfanin Air Peace ya sanar da fasinjojinsa cewa kamfanin ya yanke shawarar kin tashi ne saboda matsalar yanay.

A ranar Laraba, Babban Jami’in Hukumar Air Peace, Allen Onyema, ya ba da umarnin soke zirga-zirgar jiragen sama a fadin kasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here