Shugaban kungiyar gwamnonin Kudu-maso-Yamma kuma gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya ce tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigo a jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya cancanci ya jagoranci Najeriya.
Akeredolu ya kara da cewa Tinubu yana yin iya kokarinsa a matsayinsa na jagoran yankin Kudu maso Yamma.
Ya yi magana ne a madadin takwarorinsa yayin ziyarar da sukai kai gidan Tinubu a Bordillion a Ikoyi, Jihar Legas, a ranar Talata.
Ya ce gwamnonin yankin sun yi mubaya’a da shugabancin tsohon gwamnan jihar Legas.
Akeredolu, wanda ya jagoranci takwarorinsa zuwa taron, ya bayyana cewa, Tinubu ba wai jagoran Kudu-maso-Yamma ba ne kadai, shi ne kadai jagoran jam’iyyar APC na kasa a Najeriya.
Duk da haka, Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti, wanda shi ma yana Legas kuma ya halarci tarurrukan da suka faru a baya, amma bai halarci ziyarar Bourdillon ba.
Akeredolu ya bayyana cewa sun yanke shawarar kai wa shugaban jam’iyyar APC na kasa ziyara ne bayan taron kungiyar gwamnonin Kudu-maso-Yamma, wanda ya gudana a Legas.
Da yake magana da manema labarai bayan ziyarar, ya ce: “Mun zo ne domin mu nuna masa soyayya da kuma gode wa Allah a madadinsa.
A cewarsa “Ya kasance yana karbar baƙi a nan. Wannan wuri ya koma kamar Makka. Muma munzo a matsayin alhazai.
“Shugaban APC na kasa daya ne. Yawancin mu a Kudu maso Yamma mun yarda da shugabancinsa kuma hakan yana nuna cewa yana yin iyakar ƙoƙarinsa don ya jagorance mu.
“Ba wai shugaban Kudu maso Yamma ne kadai ba, har ma shugaban jam’iyyar APC na kasa a Najeriya. A cewar Gwamna Akeredolu.













































