Yadda duban tsaftar muhalli na ranar Juma’a ya kasance

WhatsApp Image 2025 01 31 at 14.40.28 750x430

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana rashin gamsuwarta da yadda ake fama da matsalar zubar da shara a wasu asibitocin jihar tare da bayar da wa’adin tsaftace su cikin gaggawa.

Kwamishinan Muhalli da Sauyin yanayi Dr Dahiru Muhammad Hashim ne ya bayyana hakan a yauJuma’a a lokacin da yake zagayen sanya ido kan aikin tsaftace muhalli na karshen wata da aka gudanar a ofisoshin gwamnati da ma’aikatu da tashoshin motoci da kasuwanni.

Kwamishinan ya lura da gagarumin gibi da ake da shi wajen sarrafa shara, inda ya jaddada bukatar daukar matakin gaggawa.

“Mun yanke shawarar yau za mu ziyarci wasu asibitocinmu da ke Kano domin tantance ingancin muhallinsu. Mun ga wasu wurare a cikin wani yanayi na rashin tsafta,” in ji shi.

“Manufarmu ita ce mu tabbatar da cewa mutanen da ke zuwa neman magani ba sa kamuwa da wasu cututtuka. Mun ziyarci Babban Asibitin Waziri Shehu Gidado, Bachirawa, asibitin kwararru na Murtala Muhammad da na Abdullahi Wase domin tantance yanayin tsaftar su, musamman ma bandakunansu, da kewayen su, da wuraren zubar da shara.”

Zamu kawo karshen zubar da shara ba bisa ka’ida ba a Kano- Kwamishinan muhalli

Dakta Hashim ya yi Allah wadai da rashin tsaftar muhalli a wasu asibitocin gwamnati, yana mai bayyana su a matsayin abin da ba za a amince da su ba.

“Ba na bukatar in ambaci sunaye, amma abin da muka gani a wasu wurare sam ba za a yarda da shi ba. Mun ba su sanarwar gyarawa inda muka umarce su da su gyara matsalolin cikin mako guda,” inji kwamishinan.

Ya kuma soki yadda wasu asibitocin ke fitowa fili suna kona sharar da suka hada da sharar magunguna, ba tare da tantance su ba.

A nata martanin, babbar daraktar kula da lafiya a asibitin koyarwa na Abdullahi Wase, Farfesa Hadiza Sa’id Bala, ta bayyana jin dadinta da ziyarar da kwamishinan ya kai asibitin.

Hajiya Hadiza ta ce “Za mu ninka kokarinmu na inganta tsaftar muhalli da kuma tabbatar da cewa asibitin ya kasance mai tsabta,”.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here