Annobar Ebola ta tilasta saka dokar kulle a Uganda

FB IMG 16659146215275664
FB IMG 16659146215275664

Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya saka dokar kulle ta mako uku a wasu gundumomi biyu da cutar Ebola ta shafa.

Za a rufe wuraren shan barasa da na rawa da kuma na bauta a Mubende da Kassanda.

Kazalika, za a hana motocin haya shiga da fita gundumomin, motocin da ke ɗauke da kayayyaki za a bari su shiga.

Wakiliyar BBC ta ce haka kuma shugaban ya saka dokar taƙaita zirga-zirga da za ta soma aiki daga 7:00 na yamma zuwa 6:00 na safe a gundumomin biyu.

Aƙalla mutum tara ne aka tabbatar da rasuwarsu sakamakon Ebola a ƙasar tun bayan bullarta a wannan karon.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here