Ƙungiyar marubutan Labaran Wasanni ta ƙasa (SWAN) ta kafa kwamitin shirya bikin raba kyaututtukan cika shekara 60

SWAN

Ƙungiyar Marubuta Labaran Wasanni ta Najeriya (SWAN) ta sanar da kafa wani kwamitin ƙasa domin shirya bikin bada kyaututtuka na zagayowar cikar ƙungiyar shekaru 60 da kafuwa.

Kyaututtukan za su karrama mutane da kungiyoyin da suka bayar da gudunmawa wajen ci gaban wasanni da walwalar al’umma a Najeriya.

Rahoton kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya bayyana cewa bikin bada kyaututtukan na daga cikin muhimman abubuwan da aka tanada a bikin zagayowar cika shekaru 60 da SWAN a matsayin ƙungiyar umbrella ta marubutan wasanni a ƙasar nan.

A wata sanarwa daga sakatariyar ƙasa ta SWAN, ta bayyana cewa kwamitin zai naɗa waɗanda suka cancanci samun lambar yabo tare da tabbatar da gudanar da dukkan tsare-tsare cikin tsarin da doka ta ƙungiyar ta tanada.

Karanta: Yanzu-yanzu: Ɗan wasa Dambele ya lashe kyautar Gwarzon ɗan wasan Duniya ta Ballon d’Or

Sakataren ƙasa na SWAN, Jakada Ikenna Okonkwo, a cikin takardun naɗin da aka aikawa mambobin kwamitin, ya tabbatar da naɗin tsohon sakataren SWAN na jihar Kano, Abdulgafar Oladimeji, a matsayin shugaban kwamitin.

Sauran mambobin sun haɗa da Jibo Zakari (Arewa maso Gabas), Eche Emos (Arewa ta Tsakiya), Akintunde Akinsemola (Kudu maso Yamma), Victor Okoye (Abuja), Chigozie Chukwuleta (Kudu maso Gabas/Sakataren kwamitin), da kuma Kehinde Ken Osagiede (Kudu maso Kudu).

Kwamitin zai tabbatar da karrama fitattun mutane, hukumomin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu da suka bayar da gudunmawa ta musamman wajen ci gaban wasanni da bunƙasa al’umma a Najeriya.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here