Kungiyar Kwadago ta ƙasa NLC, ta yi Allah-wadai da matakin karin harajin kashi 50% na kamfanonin sadarwa, inda ta bukaci kamfanonin da su gaggauta dawo da tsohon farashin.
A baya dai kungiyar NLC da gwamnatin tarayya sun kafa wani kwamiti mai mutum 10 da zai tattauna kan karin kudin harajin nan da makonni biyu tare da bayar da rahoto kafin a yanke hukunci na karshe kan sabon tsarin karin kudin na sadarwa.
Duk da yarjejeniyar da aka cimma, kamfanonin sadarwa sun ci gaba da kara kudin, wanda hakan ya sa NLC ta bayar da wa’adin ranar 1 ga Maris, na rufe ayyukansu baki daya, idan ba a janye karin ba.
A cikin sanarwar da shugaban kasar Joe Ajaero da babban sakataren kungiyar Emma Ugboaja suka sanyawa hannu, bayan kammala taron kwamitin kungiyar NLC a Lokoja a ranar Talata, kungiyar ta zargi kamfanonin sadarwa da cin amana da rashin bin ka’idojin da suka dace ta hanyar aiwatar da karin kafin a kammala nazari da kwamitin mai mutane 10 ke yi.
Kungiyar ta kuma soki gwamnati kan gazawarta na kare ‘yan kasa daga cin hanci da rashawa.
A matsayin matakin farko na kin amincewa da karin, kungiyar NLC ta umurci ma’aikatan kasar nan da sauran ‘yan kasa da su kauracewa amfani da kamfanonin sadarwa na MTN, AIRTEL, da GLO a kullum tsakanin karfe 11:00 na safe zuwa 2:00 na rana daga ranar 13 ga watan Fabrairu har zuwa karshen watan Fabrairun 2025.