Tsohon Ɗan Majalisar Wakilai ya rasu

Ojougboh, tsohon, dan majalisa, rasu, neja delta
Tsohon Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Ika ta jihar Neja Delta, Dakta Cairo Ojougboh ya rasu. Wata majiya ta shaidawa SOLACEBASE cewa fitaccen ɗan...

Tsohon Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Ika ta jihar Neja Delta, Dakta Cairo Ojougboh ya rasu.

Wata majiya ta shaidawa SOLACEBASE cewa fitaccen ɗan siyasar kuma jigo a jam’iyyar APC ya rasu ne a daren ranar Laraba a lokacin da yake kallon wasan kusa da na ƙarshe na AFCON 2023 tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu.

Karanta wannan: Kuskuren da dan wasan Super Eagles ya jawo aka soke kwallo ta biyu da Najeriya ta zura

Majiyar ta ce “Lokacin da aka bawa Najeriya bugun daga kai sai mai tsaron gida ita da Afrika ta Kudu a wasan kusa da na ƙarshe na ranar Laraba a Bouake da ke Ivory Coast sai ya fadi.”

Ojougboh ya kasance tsohon daraktan ayyuka a kwamitin riƙon ƙwarya na Hukumar Raya Yankin Neja Delta NDDC.

Cikakken bayanin na nan tafe…

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here