Nnamdi Kanu zai iya ci gaba da gurfana a gaban kotu, rashin lafiyarsa ba barazana ba ce ga rayuwa – NMA ta fadawa kotu

Kanu lawye

Ƙungiyar Likitoci ta Ƙasa (NMA) ta sanar wa babbar kotun tarayya da ke Abuja cewa rashin lafiyar Nnamdi Kanu, jagoran haramtacciyar ƙungiyar da aka haramta ta Biyafara (IPOB), ba matsala ce mai barazana ga rayuwa ba.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa alkalin kotun, Mai shari’a James Omotosho, ne ya umarci ƙungiyar NMA ta kafa kwamiti domin bincika sahihancin halin lafiyar Kanu, sakamakon sabanin rahotannin da likitocin hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da na lauyoyin Kanu suka bayar.

A cewar rahoton da tawagar lauyoyin gwamnati ƙarƙashin jagorancin Adegboyega Awomolo ta gabatar wa kotu a ranar 13 ga Oktoba, kwamiti na likitoci ya bayyana cewa rashin lafiyar da Kanu ke fama da ita, ba ta barazana ga rayuwarsa, kuma yana cikin koshin lafiya don ci gaba da fuskantar shari’a.

Bayan wannan rahoto, kuma babu wani ƙalubale daga bangarorin lauyoyin da ke shari’ar, inda mai shari’a Omotosho ya bayyana cewa kotu ta gamsu da cewa Nnamdi Kanu zai iya ci gaba da shari’ar da ake yi masa.

Alkalin ya bayar da umarni cewa Kanu zai samu kwana shida a jere, daga ranar 23 ga Oktoba, domin gabatar da kare kansa a kotu.

Haka kuma, ya amince da buƙatar lauyoyin Kanu ƙarƙashin jagorancin Kanu Agabi, domin su samu damar yin shawarwari da wanda suke karewa a waje da harabar hukumar DSS.

Mai shari’a Omotosho ya amince cewa wannan ganawar za ta gudana a cikin ɗakin kotu a ranar 22 ga Oktoba, daga ƙarfe 9 na safe zuwa 12 na rana, kuma ba wanda zai halarta sai Kanu da tawagar lauyoyinsa.

Shari’ar kuma za ta ci gaba da gudana daga ranar 23 ga Oktoba.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here