Tinubu ya ƙaddamar da sabbin ayyuka a Masallacin Sultan Bello, Kaduna

images 15

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu a ranar Juma’a ya kaddamar da wasu sabbin ayyuka a Masallacin Sultan Bello dake Kaduna, waɗanda Kamfanin tabbatar da tsaro na Tantita (TSSNL) ya ɗauki nauyin gina su.

Ayyukan sun haɗa da gina cibiyar yin alwala ta zamani, bandakuna 50 da suka haɗa da na musamman (VIP), da kuma tankin ruwa mai ɗaukar lita dubu 300 da aka tanadar domin amfani da masallacin da kuma al’ummar Ungwan Sarki da ke kewaye.

Tinubu, wanda ya halarci ɗaurin auren ɗan tsohon gwamnan Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, ya yaba da aikin, inda ya bayyana shi a matsayin alamar haɗin kai da kuma nuna alhakin jama’a daga bangaren masu kamfani.

Karin labari: Kaduna: Tinubu ya ziyarci iyalan marigayi Shugaba Buhari

Kafin wannan gini, masallacin na da ƙaramin wurin alwala wanda bai wadatar da ɗumbin jama’a, musamman a lokutan Juma’a.

Sabuwar cibiyar dai tana iya sauya alwalar mutane 300 a lokaci guda, yayin da tankin ruwan zai tabbatar da wadataccen ruwa ga masallacin da al’umma.

Kamfanin Tantita, ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban ’yan tawaye na Niger Delta, Cif Government Ekpemupolo (Tompolo), ya fi shahara wajen tsaron bututun mai a yankin Niger Delta.

Injiniyan aikin, Malam Abba Mubashir, ya bayyana cewa aikin ya cika bisa ka’ida daga tushe har zuwa ƙarshe, inda ya tabbatar da cewa wurin alwalar ya wadatu, kuma ruwan yanzu na isa masallacin da kewaye.

Babban Ladan na Masallacin Sultan Bello, Malam Abdurrahman Abdulhamid, ya gode wa kamfanin bisa kammala aikin da aka bari tsawon shekaru.

Ya ce aikin farko tsohon mai tallafa wa jama’a, Jack Rich, ne ya fara shi amma aka bari, inda ya roƙi Allah ya saka wa kamfanin da alheri tare da kiran ci gaba da irin wannan gudummawa.

Haka kuma, Mubashir ya bayyana cewa Tantita ta taimaka da makamantan ayyuka a wasu sassan Kaduna, ciki har da ginin makarantar Musulunci a Ambushia da kuma makarantar Kirista a Sabo.

Mazauna Ungwan Sarki sun bayyana farin ciki da aikin, inda suka ce ya zo a daidai lokacin da ake fama da ƙarancin ruwa a yankin.

Wannan kaddamarwar na daga cikin manyan abubuwan da suka haskaka ziyarar shugaban ƙasa a Kaduna, tare da ƙarfafa shiga tsakanin masu zaman kansu wajen samar da ababen more rayuwa a ƙasar.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here