Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC ta yi watsi da shirin gwamnatin tarayya na daidaita farashin wutar lantarki ga kwastomomin kamfanonin A, B da C.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi bayan taron majalisar zartarwa ta kasa a Yolan jihar Adamawa, kungiyar kwadago ta sha alwashin jagorantar zanga-zangar da za a yi a fadin Najeriya idan har gwamnati ta ci gaba da shirinta.
Karanta: TUC ta ki amincewa da karin kashi 65% na kudin wutar lantarki
A ranar Alhamis din da ta gabata, Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce za a daidaita farashin karami zuwa Band A.
A cikin sanarwar da ta fitar mai dauke da sa hannun Babban Sakataren NLC, Emmanuel Ugboaja, kungiyar kwadagon ta yi watsi da matakin.