Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya ta sanar da cewa za a sami gajimare mai kura da hadari a sassa daban-daban na ƙasar daga ranar Litinin zuwa Laraba, inda ta shawarci jama’a su kasance cikin shiri su kuma kiyaye dokokin tsaro.
A cikin hasashen da hukumar ta fitar ranar Lahadi a birnin Abuja, ta bayyana cewa za a sami ɗan gajimare mai kura a jihohin Katsina, Kano, Jigawa, Yobe, Borno da kuma wasu sassan jihar Kaduna a ranar Litinin, yayin da ake sa ran yanayi mai rana a sauran yankunan Arewa.
Hukumar ta bayyana cewa ana sa ran samun hadari a sassan kudu maso gabas musamman Taraba da yamma, yayin da yanayi mai rana da gajimare kadan zai mamaye yankin tsakiyar ƙasar.
Hakanan an yi hasashen samun hadari a wasu sassan jihohin Benue da Kogi a rana ɗaya, yayin da yankin kudu zai kasance cikin yanayi mai gajimare da yiwuwar ɗan ruwan sama a safiya.
Hasashen ya kuma nuna yiwuwar hadari da ɗan ruwan sama a wasu sassan jihohin Ogun, Cross River, Akwa Ibom, da Legas da kuma ruwan sama mai matsakaici a wasu sassan kudu maso yamma da kudu maso gabas da yamma.
A ranar Talata kuma, hukumar ta yi hasashen yanayi mai rana da gajimare a Arewa, da yiwuwar hadari a kudu maso gabas, yayin da jihohin Kogi, Benue, da Kwara za su iya samun ɗan hadari daga baya.
A ranar Laraba, hukumar ta hasashen yanayi ta yi nuni da cewa za a sami yanayi mai rana a Arewa da gajimare a tsakiya, sannan daga baya a sami hadari da ɗan ruwan sama a wasu yankuna.
Hukumar ta shawarci direbobi da sauran mazauna su kula da tuki a lokacin hadari ko kura saboda yuwuwar rage gani, sannan ta ba da shawara ga masu asma da sauran matsalolin numfashi su guji fita a lokacin kura.
Haka kuma, ta umurci kamfanonin jiragen sama su nemi rahoton yanayi na filayen sauka daga hukumar don guje wa jinkiri ko rikicewar tashi da sauka.
Ta kuma bukaci jama’a su kasance suna bibiyar sabbin bayanai da hasashen yanayi ta shafinta na yanar gizo da sauran tashoshin sada zumunta.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN.













































