Natasha ta maka Nwaebonyi kotu tana buƙatar diyyar Naira biliyan 5 saboda kalaman batanci

Untitled design 1
Untitled design - 1

Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta kai karar abokin aikinta, Sanata Onyekachi Nwaebonyi, mai wakiltar mazabar Ebonyi ta Arewa ta tsakiya a gaban kotu kan zargin bata mata suna.

karar da Akpoti-Uduaghan ta shigar ta hannun lauyanta, Michael Numa, a babban kotun birnin tarayya Abuja, na neman bayyana kalaman karya da rashin gaskiya da Nwaebonyi yayi a wata hira da yayi da gidan Talabijin na Channels a ranar 6 ga Maris, 2025.

A cewar karar, Akpoti-Uduaghan ta tabbatar da cewa Nwaebonyi ya bayyana ta a matsayin “Makaryaciya, kuma mai ɓatanci” yayin hirar.

Daga cikin bukatun, ta roki kotu da ta bayyana ikirarin a matsayin karya, da batanci cewa ita uwa ce mai ‘ya’ya shida.

Ta bayyana cewa irin wadannan kalamai na bata mata suna a matsayin abin koyi ga mata masu burin shiga siyasa.

Akpoti-Uduaghan a cikin karar ta ce kalaman Nwaebonyi sun jawo mata babbar illa ga mutuncinta da kuma kunyata ta a cikin jama’a.

Sanatar ta ci gaba da neman umarnin kotu da ya hana Nwaebonyi yin wasu munanan kalamai a kanta.

Bugu da kari, ta roki kotun da ta umurci Nwaebonyi da ya biya Naira biliyan 5 a matsayin diyya mai tsauri da kuma abin koyi ga maganganun karya, mugunta, da munanan kalamai da ya yi mata.

Ta kuma bukaci kotu da ta tilastawa Nwaebonyi da ya janye kalaman batanci a wannan dandali da yayi hirar da bayar da uzuri.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here