Tsohon mataimakin gwamnan Jihar Kogi, Edward David Onoja, ya bayyana cewa tsohon gwamna Yahaya Bello ya shafe shekaru huɗu yana gaya masa zai gaje shi a matsayin gwamna, amma sai kwana ɗaya kafin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC ya sauya shawara.
Onoja ya yi wannan bayani ne a wata hira da ya yi a MIC ON Podcast, inda ya ce Bello da kansa ne ya rika ƙarfafa shi da cewa zai zama magajinsa, shi kuma ya shiryawa hakan.
Ya ce maimakon haka, gwamnan ya bai wa lambobin majalisarsa su bakwai damar sayen fom ɗin takara, amma daga ƙarshe ya nuna goyon bayansa ga Ahmed Usman Ododo, wanda yanzu ya zama gwamna.
A cewarsa, Bello ya sanar da shi canjin ra’ayinsa kwana ɗaya kafin zaɓen fidda gwani, abin da ya karɓa cikin ladabi duk da cewa ya ji haushi.
Onoja ya ce ya gaya wa Bello: “Kai ne shugabanmu, abin da ka gani shi muke gani, amma kar ka yi kuskure.”
Ya ƙara da cewa duk da haka ya tsaya tsayin daka wajen ganin dan takarar jam’iyyar, Ododo, ya yi nasara a zaɓen gwamna na Kogi, wanda daga baya ya gaji Bello.











































