Ministan sufuri, Sanata Saidu Alkali, ya yi murabus daga majalisar ministocin shugaba Bola Tinubu, kamar yadda ofishin yada labarai na fadar shugaban kasa ya bayyana a yammacin ranar Talata.
Murabus din ya zo ne sa’o’i kadan kafin wa’adin ranar 31 ga Maris, 2026 da shugaban kasa ya sanya wa dukkan mukarraban gwamnati da ke son tsayawa takara su sauka daga mukamansu.
Alkali, wanda ya fito daga jihar Gombe, ya sanar da matakin nasa ne bayan ganawa da shugaba Tinubu a fadar shugaban kasa a daren Talata.
Ana sa ran tsohon ministan zai tsaya takarar gwamnan jihar Gombe a zaben shekarar 2027, inda yake neman maye gurbin gwamna mai ci, Inuwa Yahaya, wanda wa’adinsa zai kare a watan Mayu na shekarar 2027.
Murabus dinsa ya biyo bayan umarnin da shugaba Tinubu ya bayar ta hannun ofishin sakataren gwamnatin tarayya a ranar 17 ga Maris, 2026, wanda ya bukaci dukkan mukarraban gwamnati da ke da burin tsayawa takara su ajiye mukamansu kafin ko a ranar 31 ga Maris.
Wannan umarni ya dogara ne da tanadin sashe na 88(1) na dokar zabe ta shekarar 2026, wanda ya wajabta wa mukarraban gwamnati irin su ministoci, masu ba shugaban kasa shawara, da shugabannin hukumomi su sauka daga mukamansu kafin shiga zaben fidda gwani ko neman takara.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta tsara gudanar da zaben fidda gwani tsakanin ranar 23 ga Afrilu zuwa 30 ga Mayu, 2026, tare da gabatar da sunayen ‘yan takara kafin watan Yuli da Agusta domin shirye-shiryen zaben shekarar 2027.













































