Kotun Tarayya da ke zamanta a Kaduna ta dage sauraron bukatar beli da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya gabatar zuwa ranar Laraba.
Alkalin da ke jagorantar shari’ar, Mai shari’a Rilwanu, ya riga ya sanya ranar 31 ga Maris domin sauraron bukatar belin bayan ya saurari muhawara daga bangaren masu kare wanda ake kara da kuma masu gabatar da kara.
An gurfanar da El-Rufai a gaban kotu ta hannun Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa mai zaman kanta ICPC bisa tuhume-tuhume guda goma da suka shafi zargin karkatar da kadarorin gwamnati da kuma safarar kudade.
Tsohon gwamnan ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa.
Haka kuma, El-Rufai ya gurfana a gaban babbar kotun jihar Kaduna kan wasu zarge-zarge da suka hada da amfani da mukami ba bisa ka’ida ba, damfara da kuma niyyar aikata damfara.
An gabatar da karar ne a kansa da wani Amadu Sule (LEDA) tare da amfani da lambar shari’a KDH/KAD/ICPC/01/26.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa El-Rufai ya isa harabar kotu da misalin karfe 9:40 na safe tare da jami’an ICPC, yayin da aka tsaurara matakan tsaro a fadin birnin Kaduna, inda aka jibge jami’an ‘yan sanda, DSS da kuma na rundunar tsaro ta jihar a wurare daban-daban domin tabbatar da tsaro.











































