Zargin Almundahanar Naira Biliyan 2.4: Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da tsohuwar ministar sufurin jiragen sama Stella Oduah

Stella oduah final 0 1

Gwamnatin Tarayya a ranar laraba ta gurfanar da tsohuwar ministar sufurin jiragen sama Stella Oduah a babbar kotun Abuja kan zargin Almundahanar da ya kai Naira Biliyan 2.4.

An gurfanar da ita tare da Gloria Odita kan tuhume-tuhume guda biyar da suka shafi zargin Almundahana, karɓar kuɗi ta hanƙoron karya da kuma karya amanar aiki.

Masu gabatar da ƙara sun bayyana cewa a watan janairu 2014 Oduah da Odita sun haɗa kai wajen karɓar jimillar Naira Biliyan 2.469 daga ma’aikatar sufurin jiragen sama ta tarayya ta hannun kamfanonin Broad Waters Resources Nigeria Ltd da Global Offshore Marine Ltd bisa kakababben ikirarin aikin kulawa da fasaha da tsaro.

Gwamnati ta ce a ranar 13 ga janairu 2014 an karɓi Naira Miliyan 839.780.738.90 bisa ikirarin kudin kulawar fasaha, sannan a ranar 12 ga fabrairu 2014 an ƙara karɓar Naira Biliyan 1.629.250.000 ta hannun Global Offshore Marine Ltd kan aikin tsaro da tallafin ayyukan jiragen ruwa duk kuwa da cewa wannan ikirari ba gaskiya ba ne.

Karanta: EFCC ta tsare tsohon AGF Abubakar Malami kan zargin daukar nauyin ta’addanci da batun kuɗaɗen Abacha da aka dawo da su

A cikin ƙarin tuhume-tuhume, gwamnatin tarayya ta zargi Oduah da karkatar da kuɗaɗen da aka ware don kwangilar kamfanin 1-Sec Security Nigeria Ltd ta hanyar amincewa da sauya maƙudan kuɗin zuwa wasu asusu, abin da ya saba wa dokar amanar aiki.

Masu ƙara sun bayyana cewa laifukan sun sabawa dokokin yaudarar samun kuɗi, yayin da ita da abokiyar tuhumarta ta musanta laifin.

Lauyoyin su biyu suka nemi a ba su beli, kuma alkalin kotu Hamza Mu’azu ya bayar da beli bisa sanin kansu tare da umarnin miƙa dukkan takardun tafiye-yafiye da kuma neman izinin kotu kafin duk wata tafiya, sannan ya dage shari’ar zuwa 12 ga fabrairu domin ci gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here