Kwale-kwale ya kife da ‘yan ci-rani a tekun Libya

334814174 1593196864492513 8025525509925933246 n
334814174 1593196864492513 8025525509925933246 n

Kusan mutum 30 ne ake fargabar sun ɓace bayan da wani kwale-kwale ɗauke da ‘yan ci-rani ya kife a gaɓar ruwan Libya.

Wata ƙungiyar agaji mai suna ‘Alarm Phone’ ta ce mutanen za su iya rayuwa muddin ƙasashen Turai ba su yanke shawarar barinsu su nutse ba.

Ƙungiyar agajin ta ‘Alarm Phone’ ta ce ita ce ta farko da ‘yanci ranin suka tuntuɓa a ranar Asabar inda suka shaida mata halin da suke ciki na cewa akwai yiwuwar jirgin nasu ya kife.

To sai dai nan take ta sanar da mahukuntan Libya, to amma sai suka shaida mata cewa masu tsaron gaɓar tekun Italiya ne za su shirya duk wani aikin ceto.

Masu tsaron gabar tekun Italiya sun ce jirgin ruwan na daidai yankin da ake iya ceto mutane idan sun nutse.

To amma kuma kai wa ga waɗanda ke cikin kwale-kwalen zai zamo abu mai wuya saboda yanayi maras kyau.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here