Hotuna: Gobara Ta Kune Shaguna A Kasuwar Singer dake Kano

1678706855685
1678706855685

An wayi garin ranar Litinin da gobara a Kasuwar Singer, wadda ta shahara wajen sayar da kayan abinci a Jihar Kano.

Shaidu sun bayyana cewa gobarar ta tashi a cikin tsakar dare kuma har zuwa wayewar garin Litinin ba a gana shawo kan wutar ba.

Jami’an kashe gobara na kokarin shawo kan wutar wadda hotuna suka nuna yadda take ci gaba da ci a sassan kasuwar.

Wasu daga cikin ’yan kasuwar na kokarin kwashe abin da za su iya na daga dukiyarsu da ya rage a Kasuwar Singer.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here