Kaduna: ‘Yan sanda sun gayyaci El-Rufai, da wasu shugabannin jam’iyyar ADC

El Rufai of Kaduna State

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta gayyaci tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, da ya gurfana a gabanta, bisa zarginsa da laifin hada baki, tada hankalin jama’a, da barna, da kuma haddasa munanan raunuka.

Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da binciken manyan laifuka, Zubairu Abdullahi ne ya gayyaci El-Rufai tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) reshen jihar Kaduna.

A cikin wasikar gayyatar, El-Rufai da sauran shugabannin ADC da suka hada da Shugaban Jam’iyyar na Arewa maso Yamma, Ja’afaru Sani, ‘yan sanda sun gayyace su domin amsa tambayoyi kan zargin hada baki, tayar da hankulan jama’a, da kuma barna.

Mutanen su ne,” Mallam Nasir El-Rufai, Bashir Saidu, Ja’afaru Sani, Ubaidullah Mohammed, aka Mikiya 30, Nasiru Maikano, Aminu Abita, da Ahmed Rufa’i Hussaini da aka fi sa ni da Mikiya”.

Sai dai ‘yan jam’iyyar ADC sun ce ba a ba su takardar gayyatar ‘yan sanda ba, kuma sun karanta ne kawai a shafukan sada zumunta.

Karin karatu: ‘Yan sanda sun tabbatar da mutuwar tsohon Sufeto Janar Solomon Arase

A ranar Asabar din da ta gabata ne wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka tarwatsa taron kaddamar da kwamitin mika mulki na gamayyar jam’iyyun adawa a karkashin jam’iyyar ADC a jihar Kaduna.

Maharan dauke da makamai Irin su kulake, da duwatsu, sun far wa mahalarta taron tare da lalata kadarori.

Gamayyar ta kunshi jama’a daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) masu adawa da shugabancin jihar, tare da jam’iyyar PDP, Social Democratic Party (SDP), New Nigeria Peoples Party (NNPP), Labour Party (LP), da ADC.

Duk da faruwar lamarin, an ci gaba da gudanar da bikin rantsar da shi a cikin yanayi mai wuyar gaske. Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ta zargi El-Rufai da laifin faruwar lamarin.

Kakakin ta, DSP Mansir Hassan, ya ce tsohon gwamnan ya gaza sanar da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro game da taron, duk da gargadin da aka sha yi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here