Tsohon Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Solomon Arase, ya mutu.
Arase, mai shekaru 69, an sanar da cewa ya rasu a ranar Lahadi a asibitin Cedar Crest da ke Abuja.
Majiya daga iyalan mamacin ta tabbatar da mutuwarsa ga gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi a wata tattaunawa ta wayar tarho.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Muyiwa Adejobi, shi ma ya tabbatar da rasuwar ga gidan talabijin na Channels.
Ya ce nan ba da jimawa ba hukumomin ‘yan sanda za su fitar da sanarwa kan lamarin.
Arase, wanda ya zama Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya na 18, daga baya an nada shi shugaban hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC).
Kafin ya zama IGP, ya shugabanci hukumar leken asiri da bincike ta rundunar ‘yan sanda sa babban sashin leken asiri na rundunar ‘yan sanda.
An haife shi a ranar 21 ga Yuni, 1956, a karamar hukumar Owan ta Yamma a jihar Edo, Arase ya karanci kimiyyar siyasa a jami’ar Ahmadu Bello, inda ya kammala a shekarar 1980, sannan ya shiga aikin ‘yan sanda a ranar 1 ga Disamba, 1981. Daga nan ya samu digirin digirgir a fannin shari’a a Jami’ar Benin, sannan ya yi digiri na biyu a Jami’ar Legas.
A tsawon rayuwarsa ya riƙe manyan mukamai da dama, ciki har da babban jami’in kula da tsofaffin ‘yan sanda da kwamishinan ‘yan sanda a jihar Akwa Ibom, da mataimakin babban sufeton ‘yan sanda mai kula da harkokin leken asiri. Ya kuma wakilci Najeriya a kasar Namibiya a karkashin wata tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, kuma ya kasance mamba a Kwalejin Tsaro ta Najeriya.
Arase ya yi ritaya daga aikin yan sanda a ranar 21 ga Yuni, 2016, bayan ya kai shekarun yin ritaya na doka. A watan Janairun 2023 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari na ya nada shi shugaban hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda, inda ya rike har zuwa watan Yunin 2024.
Ya samu karbuwa sosai saboda jajircewarsa ga jin dadin ‘yan sanda da kuma yadda ya jagoranci wajen kawo sauyi. A lokacin mulkinsa, ya gabatar da manyan tsare-tsare irin su Hukumar kai daukin gaggawa ta Intelligence Response Team da sashen amsa korafe-korafe don magance munanan dabi’un ‘yan sanda, da kuma Safer Highway Patrol, wadanda suka inganta tsaro ga matafiya a fadin kasar nan. Ko da ya yi ritaya, ya ci gaba da bayar da gudunmawar yin garambawul ga aikin ‘yan sanda, musamman ta fuskar bada tsaro yayin da zabe da lokacin tarzoma.













































