Gwamnatin jihar Kano ta bayyana damuwarta kan yadda ake ta korar ‘yan Arewa daga babban birnin tarayya Abuja zuwa Kano da sauran jihohin Arewa.
Kwamishiniyar harkokin mata, yara da nakasassu ta jihar, Hajiya Amina Sani Abdullahi, ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta rabawa manema labarai ranar Alhamis a Kano.
Ta ce gwamnatin jihar ta lura cewa a cikin makonni hudu da suka gabata, an mayar da wasu ‘yan Najeriya da dama da suka hada da ‘yan asalin Kano, Jigawa, Katsina, da Kaduna daga babban birnin tarayya Abuja zuwa Kano.
A cewarta, matakin da hukumar babban birnin tarayya Abuja ta dauka ya saba wa ‘yancin da tsarin mulki ya ba kowane dan Najeriya na zama da kuma neman abin rayuwa a kowane yanki na kasar nan, matukar ba za su kawo barazana ga zaman lafiya da tsaron jama’a ba.
Karin karatu: Gwamnatin Kano ta gargaɗi ƙungiyar tuntuɓa ACF kan sake kafa majalisar dattijai
Kwamishiniyar ta kara da cewa, rahotannin da wasu daga cikin wadanda aka kora suka yi nuni da cewa an tsare su sama da kwanaki 10 a gidan yari, kuma ana ciyar da su sau daya a kullum.
Ta bayyana wannan mataki a matsayin wulakanci da rashin mutunta al’umma da dimokradiyya.
Sani-Abdullahi ta ce gwamnatin jihar karkashin Gwamna Abba Kabir-Yusuf, ba za ta amince da wulakanci da ake yi wa ‘yan kasar ba, yana mai kira ga gwamnatin babban birnin tarayya Abuja da ta kawo karshen korar da ake yi ba bisa ka’ida ba. (NAN)













































