Jami’an karamar hukuma da aka sace a Kwara sun shaƙi iskar‘yanci

Kwara map 750x430

Ma’aikatan gudanarwa biyu na karamar hukumar Oke-Ero ta jihar Kwara, Alhaji Musibau Amuda (Daraktan Kula da Ma’aikata) da Misis Omoladun Elizabeth Arinde (Jami’ar Shari’a), wadanda aka yi garkuwa da su kwanan nan, sun samu ‘yanci.

A wata sanarwa da shugaban karamar hukumar James Fadipe ya fitar, ya ce jami’an sun dawo lafiya kuma cikin koshin lafiya.

An yi garkuwa da jami’an ne yayin da suke tafiya daga Iloffa a karamar hukumar zuwa Ilorin, babban birnin jihar a ranar Juma’ar da ta gabata.

Labari mai alaƙa: Ƴan bindiga sun yi garkuwa da wata lauya da ma’aikaciyar karamar hukuma, da wasu mutane uku a Kwara

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da cewa wasu mutane biyar dauke da makamai sun tare hanyar da ke kewayen kauyen Eleyin ta hanyar Isanlu-Isin, inda suka tare wasu motocin gida guda biyu tare da kwashe dukkan mutane bakwai da ke cikin motocin, wadanda tun farko ba a bayyana sunayensu ba.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, Adetoun Ejire-Adeyemi, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce yayin da aka kubutar da mutane biyu, har yanzu yan sanda na ci gaba da gudanar da ayyukan na ceto sauran biyar da aka yi garkuwa da su tare da cafke wadanda suka yi garkuwa da su.

Karin karatu: Tsohon alkalin babbar kotun jihar Kano mai shari’a Wada Rano ya rasu

Shugaban karamar hukumar Oke-Ero, a cikin sanarwar da ya bayar a ranar Litinin, bai bayyana yadda aka kubutar da jami’an ba, sai dai ya godewa Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq, da shugabannin kungiyar kananan hukumomin Najeriya (ALGON), jami’an tsaro, sarakunan gargajiya, da malaman addini bisa kokarinsu na ganin an sako jami’an.

Sanarwar ta ce:

“Muna mika sakon godiya da godiya ta musamman ga Allah madaukakin sarki bisa rahamarsa da kuma kariyarsa bisa babban daraktanmu na kula da ma’aikata Alhaji Musibau Amuda da kuma jami’in shari’a na karamar hukumar Barista Omoladun Elizabeth Arinde wadanda suka dawo mana cikin koshin lafiya, wannan hakika Ubangiji ya yi, kuma muna cike da farin ciki da godiya.

“Muna matukar godiya ga Maigirma Gwamnan Jihar Kwara, Malam Abdulrahman Abdulrazaq, CON, da shugabannin ALGON bisa jajircewar da suka ba mu hadin kai a wannan lokaci mai cike da kalubale, muna kuma mika godiyarmu ga shugabannin addini, sarakunan gargajiya, jami’an tsaro, shugabannin siyasa, ‘yan jam’iyya, kungiyoyin DPM da LGT, da dukkan masu hannu da shuni da suka tsaya tare da mu, da addu’a.

“Allah Madaukakin Sarki Ya ci gaba da yi muku albarka baki daya, mun ci gaba da yin aiki tare domin ci gaba da samun zaman lafiya, ci gaba, da ci gaban kananan hukumominmu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here