Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar Koli ta harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), Mai Martaba Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ayyana ranar Talata 29 ga Afrilu, 2025 a matsayin ranar farko ta watan Zulki’ida 1446 bayan hijira.
Wannan sanarwar ta fito ne a cikin wata sanarwa da Wazirin Sokoto kuma shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na majalisar Sarkin Musulmi Farfesa Sambo Wali Junaidu ya fitar a ranar Litinin.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Sanarwar ta biyo bayan rashin samun wani rahoto mai kyau daga kwamitin ganin wata na kasa da kuma kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na Majalisar Sarkin Musulmi dangane da ganin jinjirin watan a ranar Lahadi, 27 ga Afrilu, 2025.
“Saboda haka, Litinin, 28 ga Afrilu, 2025, za ta kasance 30 ga Shawwal 1446, yayin da Talata 29 ga Afrilu, 2025, za ta kasance a hukumance farkon Zulki’ida 1446”.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, Sarkin Musulmi ya mika sakon fatan alheri ga al’ummar Musulmi, ya kuma bukace su da su ci gaba da yi wa kasa addu’ar zaman lafiya, hadin kai, da ci gaba.