Hukumar kula da yanayi ta kasa NiMet, ta yi hasashen samun ruwan sama da tsawa daga yau Laraba zuwa jibi Juma’a a fadin kasar nan.
Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wani rahoto da ta fitar a daren jiya Talata a birnin tarayya Abuja, inda ta ce, wasu sassan jihohin Taraba da Kaduna da kuma Adamawa za su fuskanci wannan yanayi a yau Laraba.
Haka kuma, rahoton ya bayyana cewa, jihohin su ma jihohin Kebbi da Zamfara da Katsina da Kaduna da Sokoto sai Gombe da Bauchi da kuma nan Kano, duk za su fuskanci mamakon ruwan saman da kuma tsawa.
Haka kuma hukumar, ta bayyana cewa, a yankin Arewa ta tsakiyar kasar nan ma jihohin Benue da Kwara da Neja da Nasarawa da kuma Birnin tarayya Abuja su ma duk za su fuskanci yanayin.
Hukumar, ta kuma ja hankalin al’umma da su guji yin tukin ababen hawa a yayin da ake tafka ruwa tare da kashe kayakkain lantarki daga jikin Soket tare da kaurace wa tsayawa ko kuma fakewa a karkashin bishiyu.
Haka kuma, hukumar ta NiMet ta shawarci hukumomin lura da sifurin jiragen sama da su tabbatar da daukar matakan da suka dace.













































