Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da kwamitin kwararru da zai gudanar da bincike bisa gobarar da ta tashi a Kasuwar sayar da wayoyi ta Farm Center da ke Kano, tare da abubuwan da suka faru na tallafi bayan iftila’in.
SolaceBase ta ruwaito cewa, gwamnatin ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, wadda ya fitar a daren ranar Talata.
Sanarwar ta ce, Sakataren Gwamnatin Jihar Alhaji Umar Farouk Ibrahim, wanda ya wakilci Gwamnan Jihar a wajen kaddamarwar, ya jaddada bukatar da ke akwai ta samar da tsarin bayar da agaji cikin gaskiya da adalci.
Ya kuma yi gargadin da a guji siyasantar da bayar tallafi, ya kuma bukaci duk wani taimako da za a bayar a bada ta hanyar kwamitin ko asusun da aka ware na bankin Zenith kamar haka FARM CENTER GSM Market FIRE INNCIDENCE SUPPORT FUNDS mai lamba 1310076187.
Kwamatin ya na karkashin kwamishinan ayyuka na musamman Alhaji Nasiru Sule Garo, wanda ya kunshi wakilai daga ma’aikatu da hukumomin gwamnati da hukumomin tsaro da kungiyoyin ‘yan kasuwa, da kamfanoni masu zaman kansu.
Sauran mambobin sun hada da Kwamishinan Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida da Ayyuka na Musamman sai wakilai daga hukumar kashe gobara ta jihar Kano da Ma’aikatar yada Labarai da Harkokin Cikin Gida Daraktan harkokin kudi sai Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta jiha SEMA, Rundunar ‘yan sanda da hukumar tsara birane KNUPDA da Ƙungiyar Kasuwar ta Farm Center da hukumar tsaro ta DSS kungiyar KACCIMA da kuma jami’an kananan hukumomi da masu ba da shawara na musamman da manyan masu ruwa da tsaki.













































