Lokaci ya yi da za ku cika alkawuran yakin neman zaben ku – Buhari ga zababbun gwamnoni.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga sabbin gwamnonin da aka zaba a kasar nan da su cika alkawuran da suka yi wa al’ummar kasar lokacin yakin neman zabe bayan rantsar da su mulki.

Buhari ya bada shawarar ne a cikin jawabinsa, wanda shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya gabatar a Abuja a taron kaddamar da gwamnoni, wanda kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ta shirya.

“A watan Maris na 2023, Najeriya ta karfafa tsarin dimokuradiyyar ta tare da gudanar da babban zaben sabon shugaban kasa da kuma sabbin gwamnoni 18 da aka zaba masu shigowa.

“Na yi farin cikin lura da cewa dimokuradiyya tayi halin ta kuma tana nan a raye, tana nan kuma tana ci gaba a Najeriya.

“Yayin da zabe ya kare, lokaci ya yi da za ku cika alkawuran da kuka yi a lokacin yakin neman zabe,” in ji shi.

Buhari ya ce nan da ranar 29 ga watan Mayu za a rantsar da gwamnonin da za su gudanar da harkokin Jihohinsu na tsawon shekaru hudu masu zuwa.

Ya bukace su da su dauki nauyin da ya rataya a wuyansu dan tabbatar da amanar da masu zabe suka ba su bayan shekaru hudu.

Buhari ya umarci kungiyar gwamnonin da ta inganta kyawawan manufofin da za su magance kalubalen dimokuradiyya da mulkin kasar a yau.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here