Harin Borno: Gwamnatin Tarayya ta tura karin kayan yaki da karin sojoji bisa bayanan sirri – Shettima

Kashim Shettima new 750x430

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta tura karin kayan aikin yaki na musamman da kuma karin sojoji bisa bayanan sirri zuwa yankunan da hare-haren ‘yan ta’adda na baya-bayan nan suka shafa a jihar Borno.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Shettima ya tabbatar da cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba za ta razana da irin wadannan munanan ayyukan da ya kira na tsoratarwa ba, wadanda ya ce yunkuri ne marar makoma na kokarin dagula zaman lafiyar kasa.

Mataimakin shugaban kasar ya sake jaddada cewa gwamnati na nan daram wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.

Ya ce abubuwan da suka faru a ‘yan kwanakin nan na nuna irin barazanar da har yanzu ke nan a kasa, amma ya jaddada cewa al’umma za su zabi haske maimakon duhu, da kuma fata maimakon yanke kauna.

A cewarsa, Shugaba Bola Tinubu ya samu cikakken bayani kan lamarin kuma ya bayar da umarnin gaggauta tattara dukkanin karfin tsarin tsaro na kasar domin daukar mataki.

Shettima ya ce gwamnatin tarayya ba za ta amince da wani wuri da zai zama mafakar wadanda ke son korar jama’a daga gidajensu ko kuma kwace ko da wani yanki na kasar Najeriya ba.

Ya kuma tabbatar da cewa wadanda suka aikata wadannan munanan laifuka za su fuskanci cikakken hukuncin doka.

A cewarsa, ba wai kawai yaki ake yi ba ne, illa kare mutuncin bil’adama daga wadanda ke yada sakon kiyayya da tashin hankali.

Ya kara da cewa zukatan gwamnati da al’umma na tare da iyalan jaruman sojojin da suka rasa rayukansu yayin da suke bakin aikinsu.

Shettima ya kuma ce gwamnatin nan ba za ta huta ba har sai an kubutar da dukkan mutanen da aka sace domin su koma ga iyalansu lafiya.

Ya yabawa juriyar al’ummar Borno da gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Babagana Zulum, tare da jinjina jarumtakar sojojin da ke kan gaba wajen yaki.

Shettima ya ce Najeriya kasa daya ce mai makoma daya, yana mai jaddada cewa darajar rayuwar dan Adam ba abu ne da za a yi sulhu a kai ba.

Ya kara da cewa za a kawo karshen wannan tashin hankali ba da kalamai kawai ba, sai da cikakken karfin gwamnatin Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here