Kano Pillars na fargabar fadawa zuwa rukuni na biyu a gasar NPFL

pillars
pillars

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars FC, na ci gaba da fuskantar kalubale na kare martabar ta gasar kwararru ta Najeriya NPFL.

Yunkurin kungiyar na ganin ta kare kanta daga fadawa zuwa rukuni na biyu, ya samu tsaiko bayan da tawagar MFM FC dake jihar Lagos ta doke ta da ci 2-1 a wasan mako na 28, a Lahadi 15 ga Mayu 2022.

Yanzu haka wasanni 10 ya ragewa tawagar da ta gwada kwanji na kare martabar ta a gasar, inda take a mataki na 19 a Jadawali da maki 29 wasanni 27 da ta fafata.

Sai dai a bangare daya kungiyar na da ragowar mintuna 11 na wasa da abokiyar hamayyar ta, ta Katsina United, da za a kammala a filin wasa na Moshood Abiola, dake birnin tarayya Abuja, da ya zama masauki ga tawagar ta Pillars a ranar Alhamis 26 ga Mayu 2022.

Wasan da kungiyar ke fatan ya zama zakaran gwajin dafi, da zata fara saka dan ba na fara samun maki da zai Kaita tsallake wa daga fadawa zuwa rukuni na biyu, a sauran wasanni 11 da suka rage a kakar wasanni ta 2021/22.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here