Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da kwamitin tattaunawa domin shawo kan barazanar yajin aikin ASUU da NASU

Morufu Tunji Alausa 678x430

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da Kwamitin Tattaunawa da kungiyar malaman manyan Makarantu ƙarƙashin jagorancin Mahmud Yayale Ahmed, domin hanzarta tattaunawa da ƙungiyoyin malaman jami’a ASUU da na ma’aikatan da ba malamai ba NASU a fadin jami’o’i, kwalejojin kimiyya, da kwalejojin ilimi.

Cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar ilimi, Boriowo Folasade, ya fitar a safiyar Talata a Abuja, ministan ilimi, Dakta Morufu-Tunji Alausa, ya ce an kafa sabon kwamitin ne domin daidaita dukkan tattaunawa a karkashin tsari guda wanda zai tabbatar da ci gaba da zaman lafiya da haɗin kai a sashen ilimi.

Ya bayyana cewa sabanin yadda aka saba a baya inda ake tattaunawa da kowace ƙungiya dabam, wannan sabon tsari zai haɗa dukkan masu ruwa da tsaki domin samun matsaya ɗaya mai dorewa da ta amfanar da kowa a fannin ilimi.

Karin labari: Malamai hudu na Jami’ar Tarayya Dutse sun shiga cikin kashi 2% na manyan masana kimiyya a duniya

Ministan ya ƙara da cewa an zaɓi mambobin kwamitin bisa la’akari da wakilcin dukkan fannoni na ilimi domin kada a bar kowa baya, tare da sanar da cewa an tanadi ofishin sirri na zamani domin sauƙaƙa musu aiki.

Ya ce taron farko na kwamitin zai gudana da karfe biyu na rana a yau Talata, 7 ga Oktoba.

Alausa ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ba da cikakken goyon bayan siyasa ga wannan tsari, tare da umartar a kammala tattaunawar cikin lokaci, cikin adalci da mutunta juna.

Ya jaddada cewa manufar gwamnati ita ce tabbatar da cewa dukkan ɗalibai suna ci gaba da karatu ba tare da tsaiko ba, wanda ya ce wannan shi ne ainihin Manufar Sabon Fatan Gwamnatinsa.

Ministan ƙwadago da aikin yi, Mohammed Maigari Dingyadi, ya yaba wa ma’aikatar ilimi bisa ɗaukar tsarin haɗin kai wajen warware matsalolin masana, inda ya ce zaman lafiya mai ɗorewa a sashen ilimi na buƙatar tattaunawa tsakanin dukkan ɓangarori.

Ya umarci mambobin kwamitin da su zama masu adalci da gaskiya a cikin aikinsu, tare da tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar da za ta kawo zaman lafiya mai dorewa.

A nasa bangaren, shugaban kwamitin, Alhaji Mahmud Yayale Ahmed, ya gode wa gwamnati bisa amincewa da su, inda ya tabbatar da cewa za su yi aiki cikin gaskiya, da haɗin kai, tare da tabbatar da cewa shawarwarin da za su bayar suna da amfani, za su iya tabbatar da kwanciyar hankali da cigaba a sashen ilimi.

Gwamnati ta jaddada aniyarta ma dawo da kwanciyar hankali da amincewa a tsarin manyan makarantu ta hanyar tattaunawa mai ma’ana da jagoranci mai ƙarfi, bisa manufar Sabon Fatan Shugaba Tinubu – inda kowane ɗalibi zai ci gaba da karatu, kowane malami ya sami daraja, kuma kowace cibiyar ilimi ta bunƙasa cikin zaman lafiya da cigaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here