Gwamnatin kasar Somaliya ta umarci kafafen yada labarai na cikin gida da su mika labarai da sauran shirye shirye ga gwamnati don tantancewa kafin wallafa su.
Rahotanni sun ce dalilin daukar wannan mataki bai rasa nasaba da tsanantar hare-haren da ake kai wa ‘yan jarida da kafofin labarai a kasar.
Mataimakin ministan yada labarai Abdulrahman Yusuf, ya ce bai san da umarni na gwamnati ba. Duk da wannan musantawar, kafofin labarai a fadin kasar sun shaidawa Muryar Amurka cewa umarnin ya fito ne daga ofishin sadarwa na fadar shugaban kasar.
Kafar yada labarai ta Risaala, daya daga cikin kafofin labaran yanar gizo tace tashoshi da yan jaridu a babban birnin Mogadishu sun ce wannan abune ba mai yiwuwa ba, saidai wata majiya ta ce makasudin sabuwar manufar tantancewa abune da ba za a iya aiwatar da su ba.
“Manufar ita ce ta tantancewa, saboda ba da umarnin ga [kafofin watsa labarai] su aika tareda keɓance abubuwan da gwamnati ba ta so.
“Saboda haka, aiwatar da shi yana da matukar haɗari ga kafofin watsa labarai na Somaliya kuma abune ba mai yiwuwa ba,” Mohammed Abdiwahab, babban darektan jaridar ya ce.
Anasa bangaren wani editan jaridar yanar gizo ta Garowe Online Abdirahman Adani, ya ce sabon umarnin “yana share hanya ga gwamnati ta rufe kafafen yada labarai masu zaman kansu, wanda a yanzu ita ce kadai amintacciyar hanyar samun labarai ga jama’a.”
Ya kara da cewa, “Wannan umarnin da alama zai hana kafafen yada labarai yada gaskiya, sannan kuma ya hana kafafen yada labaran yada labarai na son rai dakuma duk wani abu da ya saba wa manufar gwamnati.”
Wasu ‘Yan jaridu da dama dake karkashin inuwar kungiyar ‘yan jarida ta Somaliya sun nuna rashin amincewa da umarnin da aka bayar.
Mohammed Bulbul, kakakin kungiyar ya ce “Zai yi tasiri ga ‘yan jarida da kafafen yada labarai, kuma idan ba a yi watsi da su ba, to ba za a samu kafafen yada labarai ko ‘yan jarida da ke bayar da labarin gaskiya ba.”
Kungiyar ta kara da cewa “Mun yi hannun riga da gwamnati wajen aiwatar da wannan umarni, amma a shirye muke mu hada kai da gwamnati wajen inganta ‘yancin fadin albarkacin baki.”













































