Mataimakin shugaban kamfanin sifirin jiragen saman Max Airline, Alhaji Bashir Barau Mangal ya rasu.
Wata majiya mai tushe ta shaidawa jaridar Solacebase cewa Bashir Mangal ya rasu ne da sanyin safiyar Juma’a, a Abuja bayan gajeruwar rashin lafiya.
“Za a yi jana’izar Marigayin da misalin karfe 4:00 na yamma a yau a Katsina,” a cewar majiyar.
Muna tafe da cikakken rahoto nan gaba.













































