Gwamnatin jihar Bauchi ta ayyana ranar Juma’a, 28 ga Nuwamba, a matsayin ranar hutu domin girmama fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman-Bauchi, wanda ya rasu a ranar Alhamis.
A cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamna shawara kan harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar a madadin gwamna Bala Mohammed, ta bayyana cewa an tsara hutun ne domin bai wa ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu, dalibai da mazauna jihar damar halartar sallar jana’iza.
Sanarwar ta kara da cewa za a gudanar da sallar jana’izar ne da misalin ƙarfe uku na rana a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.
NAN













































