NiMET ta yi hasashen samun hasken rana da hazo na tsawon kwana 3 daga juma’a

Sunshine

Hukumar kula da  hasashen yanayi ta ƙasa NiMET ta yi hasashen cewa daga ranar Juma’a zuwa Lahadi za a samu hasken rana tare da hazo a sassa daban-daban na ƙasar nan.

A hasashen da NiMET ta fitar a Abuja, ta bayyana cewa a ranar Juma’a za a samu hazo matsakaici mai nisan gani tsakanin kilomita biyu zuwa biyar a wasu sassan Katsina, Kaduna, Zamfara da Kebbi.

Ta kuma yi hasashen hazo mai sauƙi a Kano, Jigawa, Borno, Yobe, Gombe, Bauchi, Taraba da Adamawa a duk tsawon lokacin da hasashen ya shafa.

A yankin tsakiya, ta yi hasashen hazo matsakaici mai nisan gani tsakanin kilomita biyu zuwa biyar a Neja da Babban Birnin Tarayya, yayin da a Nasarawa, Benue, Kogi da Kwara za a samu hasken rana tare da ɗan gajimare.

A yankin kudu, ta yi hasashen yanayi mai ɗan gajimare tare da yiwuwar guguwar iska mai ɗauke da ruwan sama kaɗan a Cross River, Akwa Ibom da Rivers da sassafe.

Daga baya da rana, ta yi hasashen guguwar iska mai ɗauke da ruwan sama a Imo, Abia, Ondo, Oyo, Ogun, Legas, Edo, Delta, Rivers, Bayelsa, Cross River da Akwa Ibom.

A ranar Asabar, NiMET ta yu hasashen hasken rana tare da ɗan hazo a yankin arewa.

A Neja ta yi hasashen hazo mai sauƙi, yayin da sauran yankin tsakiya za su samu hasken rana tare da ɗan gajimare.

A kudu, ta yi hasashen yanayi mai ɗan gajimare a safiya, sannan daga baya a yi rana, sannan akwai hasashen guguwar iska da ruwan sama a Delta, Ondo, Legas, Bayelsa, Rivers, Akwa Ibom da Cross River.

A ranar Lahadi, ta yi hasashen hasken rana a duk yankin kudu, inda a yankin tsakiya ta yi hasashen hasken rana tare da ɗan gajimare, yayin da kudanci zai fara da ɗan gajimare a safiya.

Daga baya da rana, ta yi hasashen guguwar iska mai ɗauke da ruwan sama kaɗan a Legas, Ogun, Imo, Abia, Edo, Delta, Bayelsa, Cross River, Akwa Ibom da Rivers.

Hukumar NiMET ta shawarci direbobi da su yi taka-tsantsan yayin tuki, tare da jan hankalin masu fama da ciwon asma da sauran matsalolin numfashi su kiyaye saboda hazo.

Haka kuma ta shawarci hukumomin jiragen sama su rika karɓar rahotannin yanayi na filayen jirage domin tsara ayyukansu yadda ya kamata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here