Gwamnatin Benue ta bawa baƙin makiyaya mako 2 su fice daga jihar

gwamnati, benue, makiyaya, jihar
Gwamnatin jihar Benue da ke arewa ta tsakiyar Najeriya, ta bai wa Fulani makiyaya da ta ce baki ne da ke kwarara cikin jihar da kuma ake zargin na dauke da...

Gwamnatin jihar Benue da ke arewa ta tsakiyar Najeriya, ta bai wa Fulani makiyaya da ta ce baki ne da ke kwarara cikin jihar da kuma ake zargin na dauke da makamai wa’adin makonni biyu su fice a jihar ko su fuskanci fushin hukuma.

Karin labari: Majalisar dattawan Najeriya ta amince kafa kwamitin kudi na CBN

Gwamnan jihar Hyacinth Alia ya kafa wani kwamiti na musamman da zai tabbatar da bin umarnin, sannan ya jaddada cewa har yanzu dokar nan da ta haramta kiwon dabbobi a sarari na ci gaba da aiki.

To sai dai kungiyar Miyetti Allah reshen jihar ta nesanta kanta da ‘ya’yanta da yin kowane hadin gwiwa da dukan wasu bata garin makiyaya a cikin jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here