Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da cikakken goyon baya ba tare da wata shakka ba ga kan dokar ta-ɓaci da ya ayyana kan tsaro kwanan nan.
Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanyawa hannu a ranar Alhamis.
A lokacin taron Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano karo na 34 da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Kano, a ranar Alhamis, Gwamna Yusuf ya yaba wa Shugaba Tinubu kan ɗaukar matakai masu ƙarfin guiwa da tsanani wajen fuskantar ƙalubalen tsaro da ke ƙaruwa a ƙasar, musamman a yankin Arewa.
Gwamna Yusuf ya kuma tattauna batutuwan tsaro na cikin gida a Jihar Kano, inda ya sake tabbatar da ƙudurin gwamnati na kiyaye rayuka da dukiyoyin mazauna jihar.
Ya nuna damuwa kan rahotannin cewa wasu ‘yan bindiga sun shiga wasu ƙananan hukumomi, musamman a cikin Yankin Kano ta Arewa, amma ya tabbatar wa al’umma cewa gwamnatin jihar, tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro, na ɗaukar matakai na gaggawa don kawar da barazanar.
Gwamna ya gode wa mutanen Kano saboda goyon baya da amincewa da suke yi wa gwamnatin, sannan ya bayyana cewa kasafin kuɗin 2026 zai inganta rayuwar talakawa sosai, tare da mayar da hankali kan ci gaban ababen more rayuwa da haɓaka ƙwarewar ɗan adam.













































