An ɗaure ma’aikacin lafiya ɗan Najeriya a Burtaniya saboda sumbatar marar lafiya

IMG 20250616 WA0018

Wata kotu a kasar Birtaniya, ta yanke wa Adewale Kudabo, ma’aikacin asibitin York, da ta samu da laifin sumabatar wata marar lafiya, daurin shekara guda a gidan yari.

Alkalin kotun, mai shari’a Alex Menary, ya ce Kudabo ya “ci amanar da aka ba shi a matsayin kwararren jami’in lafiya.

Kudabo ya amsa laifuffukan guda biyu da ake zarginsa da aikatawa a ranar farko da aka fara shari’ar sa a watan Afrilu.

Menary ya ce, wadda aka ci wa zarafin ta ce bayan sun gama yi mata wanka ne sai Kudabo ya sumbace ta a lebe.

Haka kuma ya kara da cewa, duk da majinyaciyar na cikin zafin ciwo sosai, ta yi kokarin guje wa sumbatar.

Fernnandez ya ce an bar majinyaciyar cikin rudani kuma ta ji babu dadi da lamarin.

Kwanaki bayan faruwar lamarin, Fernnandez ta kara da cewa Kudabo ya tambayi majinyaciyar ko tana son sake yi mata wanka, inda a nan ma ya sake kokarin sumbatar ta.

Jerry Sodipe, lauyan Kudabo, ya ce, ba shi da wani laifi a baya kuma ya nuna nadamar abin da ya aikata.

“Ya daga hannayensa ya ce, eh ya aikata laifi, bai kamata ya yi hakan ba,” in ji Sodipe.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here