Jihar Texas ta kai karar Google bisa bada bayanan wasu batare da izini ba

google
google

Babban Lauyan Jihar Texas dake kasar Amurka Ken Paxton ya kai karar Google bisa mika bayanan yatsun wani ba tare da izinin su ba”

Rahotannin baya bayanan ya nuna yadda miliyoyin alummar jihar Texans dasuks nuna sha’awar kasuwancin babbar kasuwar, inda ya bude kafar bada bayanan halittar yatsun su ba tare da izinin su ba.

Ofishin Babban Lauyan Paxton ya ce kunshin karar ta yi zargin kamfanin na intanet ya tattara miliyoyin kwayoyin halitta, da suka hada da sautin murya da kuma fuskoki.

“Yin amfani da bayanan sirri na Google na Al’ummun jihar Texas cin zarafin ne babba,” in ji shi.

Mai magana da yawun Google Jose Castaneda cikin wata sanarwa ta ce Google “zai shirya dukkanin bayanai kai tsaye a kotu.”

Kafofin labaran cikin gida sun rawaito cewa wadanda suka karya dokar suna fuskantar tarar dalar Amurka dubu 25 ga duk wadanda sukayi laifin.

An bayar da rahoton cewa, karar ita ce ta baya-bayan nan da wasu jihohi da dama suka shigar a kan manyan kamfanonin fasahar kere-kere a intanet.

A baya Paxton ya shigar da kara a kan Google saboda keta Dokar Kariyar Ciniki na yaudarar Mutanen Texas da kuma bin diddigin masu almundahana da yaudarar mutane ba tare da izininsu ba. (Xinhua/NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here