An samu fashewar wani abu da sanyin safiyar yau Talata a unguwar Sabon Gari da ke Kano inda ake fargabar wasu sun jikkata.
Wani ganau ya shaida wa Solacebase cewa fashewar ta faru ne a yankin Aba by Court road.
Wata majiya ta ce, wasu yara ƴan makaranta abun ya shafa yayin da fashewar ta afku a kusa da harabar makarantarsu.













































