Gamayyar Kungiyoyi Sun Sayawa Farouq Sule Garo Fom din takarar Majalisar Tarayya kan kudi Naira Miliyan 10

IMG 20220510 WA0060 608x381 1
IMG 20220510 WA0060 608x381 1

Gamayyar Kungiyoyin marawa Farouq Sule Garo sun saya masa fom din tsayawa takara domin cimma burinsa na zama Dan-Majalisar Wakilan Tarayya.

Kungiyoyin da suka hada da ‘yan mazabar sa da iyalai da abokan arziki sai kungiyoyin mata da abokan huldar kasuwanci a cikin gida Najeriya da ma kasashen ketare, sune suka tara sama da Naira miliyan 10 a karshen makon daya gabata domin siyan fom din.

Farouq, wanda ke da burin wakiltar mazabun Gwarzo da Kabo a Majalisar Tarayya, ya yi alkawarin ba zai ci amanar amincewar da aka yi masa ba matukar ya samu tikitin jam’iyyar, ya kuma yi nasara a babban zaben shekarar 2023.

“Ina mai matukar farin ciki tare da matukar mamaki, bisa wannan karramawa da mutane na suka min tare da nuna yardarsu da Kwarin gwiwarsu a kai na.” Inji Farouq.

‘’ Gudanar da managartan ayyuka ga al’ummar mu tare da daga darajar Yankin mu suna gaba cikin abubuwan da nake fatan gudanarwa idan lokaci ya yi.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here