Jam’iyyar PDP ta fara tantance ‘yan takararta 17 da suke neman shugabancin kasa a zaben shekara mai zuwa ta 2023.
Kamfanin dillancin labarai NAN ya ruwaito cewa an gudanar da tantancewar a karkashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark a Ofishin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP dake Legacy House a birnin tarayya Abuja.
‘Yan takarar 17 sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon kakakin majalisar wakilai kuma shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto.
Tsofaffin shugabannin majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki da Sanata Anyim Pius Anyim sai gwamnonin jihohin Bauchi da Rivers Bala Mohammed da Nyesom Wike da gwamnan Akwa Ibom Udom Emmanuel da kuma tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, suma suna cikin masu neman tsayawa takarar shugabancin kasar.
Sauran kuma sun hada da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose da wani likita da ke zaune a Amurka, Nwachukwu Anakwenze sai hamshakin dan jaridar nan Dele Momodu da wani ma’aikacin bankin zuba hannun jari kuma masanin tattalin arziki, Mohammed Hayatu-Deen.
Kazalika akwai wani mai harhada magunguna, Mista Sam Ohuabunwa da tsofaffin shugabannin majalisar dokokin Abia, Cosmos Ndukwe da Chikwendu Kalu da wani mai zanen taswira tare da gina gidaje, Mista Charles Ugwu sai kuma mace daya tilo da ke neman tsayawa takarar Tareila Diana.
Kawo lokacin rubuta wannan labari dai ‘Yan takarar da aka kammala tantancewa sun hada da Wike, Anyim, Atiku, Saraki, Udom, Anakwenze, Fayose da kuma Kalu.










































